Hira da Farfesa Bassey Antia | Zamantakewa | DW | 03.07.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Hira da Farfesa Bassey Antia

Amfani da kalaman da suka dace na taka rawa wajen sanyaya ran majiyata

default

Magunguna ga masu ɗauke da ƙwayoyin HIV/AIDS

Jama´a masu sauraro barkanku da warhaka, barkanmu kuma da saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na Taɓa Ka Lashe, shirin da ke duba batutuwan da suka shafi addinai, al´adu da kuma zamantakewa tsakanin al´umomi daban daban a wannan duniya ta mu.

A kwanakin baya sashen binciken kimiyya na George Forster dake ƙarƙashin gidauniyar Alexander von Humboldt a nan Jamus ya yi bukin cikansa shekaru 10 da kafuwa. Bukin wanda aka yi a nan gidan radiyon DW dake birnin Bonn ya samu halarcin masana kimiyya na fannoni daban daban da suka haɗa da siyasa, tattalin arziki, kiwon lafiya, zamantakewa da kuma harsuna daga sassa daban daban na wannan duniya ta mu. Daga cikin masana kimiyya da suka gabatar da ƙasidu a lakcocin da aka yi a gun wannan buki akwai Farfesa Bassey Edem Antia na sashen harsuna da al´adu na jami´ar Maiduguri dake tarayyar Nijeriya. Bayan bukin Farfesa Bassey Antia ya kawo mana ziyara nan sashen Hausa inda muka tattauna da shi game da aikin sa na binciken kimiyya da kuma ƙalubalen da yake fuskanta. In kun biyo a hankali a cikin shirin za ku ji yadda hirar ta mu ta kasance.

Madalla. To kamar yadda na yi muku bayani a shimfiɗar shirin a yau a gida muke wato nan sashe Hausa na DW, inda a kwanakin baya aka gudanar dabujin cika shekaru 10 da kafuwar sashen binciken kimiyya na George Forster dake ƙarƙashin gidauniyar Alexander von Humboldt a nan Jamus. Maƙasudin wannan taro da ya haɗa masana kimiyya daga ko-ina cikin duniya shi ne ba su damar musayar ra´ayoyi dangane da muhimmancin ayyukan binciken da suke yi musamman ga ƙasashensu. Ɗaya daga cikin waɗannan masana kimiyya da suka gabatar da ƙasidu a lakcocin da aka yi shi ne Farfesa Bassey Edem Antia wanda ya ce a matsayinsa na masanin harsuna da al´adu dake aiki a ɓangaren kiwon lafiya, abin da ya sa a gaba shi ne gano muhimmancin aikin da ƙwararrun masana ilimi ke yi a fannin na kiwon lafiya.

1. Ya ce “Idan ka dubi taswirar duniya a ɓangaren mutanen da ke mutuwa sakamakon cutar AIDS ko Sida zaka ga cewa Afirka ke kan gaba. A ɓangaren cututtukan da za a iya maganinsu ma Afirka ce ke a sahun gaba a yawan waɗanda ke mutuwa sakamakon waɗannan cututtuka. Saboda tambayar da masanin harsuna zai yiwa kansa ita ce ta yaya za ka iya yin amfani da ilimin da Allah Ya ba ka don gano hanyoyin magance waɗannan matsaloli?”

A saboda haka aikin Farfesa ya ta´allaka wajen gano kalamai mafi dacewa a yi amfani da su a matakan wayarwa da jama´a kai a yaƙi da cututtuka kamar AIDS ko Sida ba tare da an ƙarawa masu ɗauke da ƙwayoyin cutar wani nauyi dangane da halin da suke ciki ba. Domin sau da yawa kalaman da ake amfani da su suna mayar da hannun agogo baya a ƙoƙarin magancewa ko matakan da ake ɗauka na kiwon lafiya, wanda haka ya ke hana samun wata rayuwa mai inganci ga mutanen da ke ɗauke da ƙwayoyin cututtukan da ake son a magance su.

To shin wata alaƙa ke akwai tsakanin masanin harsuna da kuma matakan kiwon lafiya ga jama´a? Farfesa Bassey ya yi bayani yana mai cewa.

2. “Idan ana maganar kiwon lafiya ga jama´a abin da muke nufi shi ne a matsayin mu na al´umma mai za mu iya yi domin tabbatar da ɗaukar nagartattun matakan kiwon lafiya. A wannan fanni ana magana ne dangane da ilimantar da mutane game da matakan rigakafi na su yi ko kar su yi wasu abubuwa da suka saba yi bisa al´ada domin su kasance cikin ƙoshin lafiya. Tambaya a nan ita ce ta yaya za ka aike musu da wannan saƙo? Dole sai da kalamai mafi dacewa. Ka ga a nan kuwa dole sai da masanin harsuna za a samu biyan buƙata. Shi kuma a na sa ɓangare dole ne ya naƙalci harsuna ko kalaman da suka fi karɓuwa a tsakanin jama´a kana ya haɗa kai da ma´aikata a waɗannan fannoni kamar na kiwon lafiyar jama´a da muke maganarsa yanzu.”

An yi ƙiyasin cewa a wasu ƙasashen Afirka akwai harsuna daban daban. A tarayyar Nijeriya alal misali ana da al´ummomi da harsuna daban daban fiye da 300. To amma fargabar da ake nunawa ita ce yadda masu amfani manyan harsuna ke barazanar mamaye ƙananan harsuna. Shin a matsayinka na mai ilimin harsuna da akwai wani abin da ka ke yi don daƙile wannan barazana ta gushewar ƙananan harsuna domin kamar yadda aka ce duk wanda ya rasa harshensa na asali to ko shakka babu ya rasa al´adarsa ta gargajiya wato kenan kamar yadda hausawa suka ce duk wanda ya bar gida gida ya barshi?

3. “A dai halin da ake ciki muna gudanar da ayyukan bincike iri daban daban a fannin tara bayanai. Ra´ayoyin masana kimiyyar harsuna sun zo ɗaya cewa idan aka tara bayanai dangane da wani harshe ko yare, to ko da dukkan masu magana da wannan harshe sun kau to aƙalla muna da rubutattun bayanai game da wannan harshe. Yawan al´umma da ƙarfin tattalin arziki suna taka muhimmiyar rawa wajen ƙarfafa amfani da harshe ko rashin amfani da shi. Abin da ya fi zama a´ala shi ne mu yi ƙoƙarin amfani da ƙananan harsunan domin biyawa masu amfani da su muhimman buƙatunsu na rayuwa. Idan bana daraja yare na, to akwai yiwuwar zan yi watsi da shi in rungumi wani yaren wanda na ke ganin zai biya mun buƙata ta.”

Masanin ilmin harsunan na jami´ar Maiduguri ya ƙara da cewa hanya mafi dacewa wajen ƙarfafa guiwar ƙananan ƙabilu don amfani da harsunansu shi ne wallafa littattafai na makarantun firamare da sakandare a cikin harsunansu sannan a ɗauki matakan tabbatar da an yi amfani da su. Ya ce ta haka za a ba da gagarumar gundunmawa wajen ci-gaba da wanzuwar waɗannan harsuna. To sai dai ɗan Adam yana da wani ilhami na rayuwa kuma zai yi amfani da duk wata dubara ciki har da ta yare don ya rayu, inji farfesa Bassey sannan sai ya ƙara da cewa.

4. “Idan na ga wani yare zai buɗe min ƙofofin samu ai dole zan rungume shi sannan in yi watsi da waɗanda ba sa amfanar da ni da komi. To a nan ya kamata mu jaddada buƙatar da ke akwai wajen tabbatar da harsuna da dama sun zama masu inganta rayuwar mutane wato kamar samun wadata da kuma ilimi. Sai mun yi haka ne kaɗai za mu iya hana wasu harsunan mu gushewa domin kamar yadda ka faɗa ne idan yare ya gushe to mun yi asarar wani ɓangare na abin da muka gada daga kakannin kakanni. Kuma kamar yadda masana kimiyya suka duƙufa wajen kare tsirrai da sauran halittu to ya kamata mu kuma masana harsuna da sauran fannonin kimiyyar zamantakewa mu mayar da hankali wajen kare harsuna da al´adun gargaji.”