Hillary Clinton ta nuna sha´awar zama macen farko a mukamin shugabar Amirka | Labarai | DW | 21.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hillary Clinton ta nuna sha´awar zama macen farko a mukamin shugabar Amirka

´Yar majalisar dattijan Amirka kuma uwargidan tsohon shugaban kasar, Hillary Clinton ta dauki matakin farko na kaddamar da wani kamfen na zama mace ta farko a mukamin shugaban Amirka. A cikin wani sakon faifayen bidiyo aka watsa ta shafin ta na intanet, Hillary Clinton mai shekaru 59 ta gaiyaci masu kada kuri´a da su fara tattaunawa da ita akan manyan batutuwa da kasar ke fuskanka. A kuma halin da ake ciki gwamnan jihar New Mexico Bill Richardson ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasar ta Amirka. Richardson wanda shi ma dan jam´iyar democrat ne ya ce zai kafa wani kwamiti don yin duba hanyoyin samun nasararsa.