Hillary Clinton ta lashe zaben New Hamshire | Labarai | DW | 09.01.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hillary Clinton ta lashe zaben New Hamshire

A Amirka Sanata Hillary Clinton ta lashe zaben fitar da gwani na New Hamshire, kwana ɗaya bayan ƙuri’ar jin ra’ayin jama’a ya nuna cewar dan takarar jam’iyar Democrat Barack Obama na kann gaba, wanda ita Clinton ta ki amincewa da shi. A jam’iyar Republican kuwa, Sanator John MCain ya kada tsohon gwamnan jahar Massachussets Mit Romney da Mike Huckabee wanda ya lashe zaben IOWA. ɗan takara McCain mai shekaru 71 da haifuwa ya ƙarfafa kampen dinsa a ‚yan makwannin baya, a yayin da Hillary Clinton ta jami’iyar Democrat ta ƙara tashi tsaye bayan ta zo na uku a zaben IOWA.