1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hikmatyar yayi kiran ta da bore a kasar Afghanistan

April 13, 2004

Gulbuddin Hikmatyar yayi kira ga ‚yan kasar Afghanistan da su ta da kayar baya daidai da takwarorinsu a kasar Iraki

https://p.dw.com/p/Bvkm
Taswirar Kasar Afghanistan
Taswirar Kasar AfghanistanHoto: AP

Shi dai Gulbuddin Hikmatyar wani fitaccen mutum ne da Allah Yayi masa basira yana kuma da cikakkiyar masaniya a game da yadda za a iya sosa wa mutane daidai inda ke musu kaikayi domin samun goyan baya daga garesu. Babbar shaida game da haka shi ne kiran da ya gabatar na ta da bore a kasar Afghanistan da kuma goyan bayan yakin jihadi a kasar Iraki. Kamata yayi wannan fafatawar ta karfafa wa ‚yan adawa guiwa a kasar Afghanistan. Ya ce muddin mayakan Afghanistan sun yunkura to kuwa a cikin kiftawa da Bisimillah zasu fatattaki sojojin mamayen daga harabar kasarsu fiye ma da yadda lamarin yake a kasar Iraki. Gulbuddin Hikmatyar, madugun askarawan sa kai kuma tsofon P/M kasar Afghanistan dake neman an shiga tserereniya tsakanin mayakan Afghanistan da takwarorinsu a Iraki domin ganin wanda zai fara cimma nasarar fatattakar sojojin mamayen daga harabar kasarsa a tsakaninsu, yana da cikakkiyar masaniya a game da yakar sojan mamaye, domin kuwa yana daya daga cikin jigogin mayaka na Mujahideen da suka fafata da sojan mamaye na tsofuwar Tarayyar Soviet a cikin shekarun 1980. Hikmatyar, kazalika, fitaccen mayaki ne, wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen bannatar da wani bangare na birnin Kabul a cikin shekarun 1990. Ya san dukkan matakai na yada farfaganda, kuma yau kimanin shekaru biyu da rabi ke nan da yake nanata kiran gabatar da yakin jihadi akan sojojin kasa da kasa da aka dirke a Afghanistan, wadanda ya kira marasa addini. To sai dai kuma kasar Afghanistan ta banbanta da kasar Iraki. Akasarin al’umar kasar sun saka dukkan burinsu akan taimako daga ketare tun bayan kifar da mulkin kungiyar Taliban. Afghanistan bata da wasu gaggan kungiyoyi ko jami'iyyun siyasa, sai dai wasu rukunoni na ‚yan sa kai iri dabam-dabam da suka barbazu a fadin kasar. Kowane daga wadannan rukunoni da irin buri da kuma bukatun da ya sa gaba. Daga cikinsu akwai masu neman fito-na-fito, kamar kungiyar Taliban da kuma wadda Hikmatyar ke wa jagora. Sai kuma wadanda ke ba da fifiko ga sare ka noke kamar kungiyar Al-Ka’ida. Kazalika akwai wadansunsu da ke wa gwamnatin rikon kwarya ta Hamid Karzai shigo-shigo ba zurfi, inda a zahiri suke nuna mata biyayya amma a boye suke mata zagon kasa. Dukkan wadannan abubuwa ne da aka san kasar Afghanistan da su tun da jimawa. Shuagabannin yakin kasar kama daga Hikmatyar zuwa ga Rabbani da Dostum sun dade suna gaba da juna kuma tuni da yawa daga al’umar Afghanistan suka dawo daga rakiyarsu. Amma fa duk da haka tilas ne a rika sara tare da duban bakin gatari, saboda mutane irinsu Hikmatyar, ko da bai kai ga tayar da zaune tsaye ba, amma yana iya hana ruwa gudu ga matakan sake gina wannan kasa dake yankin Hindukush. Ita kanta kungiyar Taliban, tuni ta mayar da kashi daya bisa biyar na harabar Afghanistan karkashin angizonta tana kuma bakin kokarinta wajen hana ci gaban wannan yanki. Mai yiwuwa, gwamnatin Kazai, a sakamakon goyan bayan da take samu daga ketare, ba za a iya kifar da ita ba, amma kungiyoyin dake adawa da ita suna iya hana yaduwar ikonta zuwa sauran sassa na kasar Afghanistan.