Hijirar kifi mai ban mamaki | Amsoshin takardunku | DW | 02.08.2007
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Hijirar kifi mai ban mamaki

Yanda kifayen Salmon suke yin hijira

Kifayen Salmon

Kifayen Salmon

Jama’a masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, barkammu kuma da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na amsoshin takardunku,shirin da yake amsa tambayoyin da ku masu sauraro kukan aikomana.

Tambaya: Fatawar mu ta wannan makon ta fito daga hannun Malama Salamatu Malam Ali daga Jamhuriyar Niger. Malamar cewa tayi,Shin dagaske ne akwai wani kifin teku da ake kira da suna Salmon,wanda yake yin hijira daga Teku ya tafi Kogi ya yi kyankyasa, kuma daga baya ya koma Tekun da kansa?

Amsa: To da farko dai sai muce babu shakka akwai wannan kifi, kuma shi kifin Salmon wani nau’i ne na kifi da ake samunsa a Tekun Pacific. Wannan kifi yana da wadansu kebantattun siffofi, kuma wadannan siffofi anfi ganinsu yayin da yake komawa Ruwan-kogi domin kyankyasar Kwayaye.

Wadannan kifaye na Salmon, mafi yawan rayuwarsu suna yinta ne a cikin Teku, to a lokacin da suke bukatar yin kyankyasa sai su yi hijira zuwa ruwan-kogi .Lokacin da sukeyin wannan hijira , shine lokacin bazara, kuma a yayin da suka fara yin wannan tafiya , launin jikinsu Ja ne, amma kuma a karshen tafiyar launin sai ya koma Baki, to wannan shine daya daga cikin kebantattun siffofinsu.

A yayin wannan tafiya tasu sukan rika bin gefen ruwa domin su tarar da koguna , yadda zasu isa inda suke so su kyankyashe kwayayen nasu. Kuma suna isa wajen yin kyankyasar duk kuwa da irin garari da kuma barazana irin ta igiyar ruwa da kuma tambal-tambal na teku da dai su ambaliyar ruwa da dai sauran hadarurruka dake tattare da ruwan teku.

To daga farkon wannan hijira zuwa karshenta , kifayen suna cinye tafiyar da ta kai daga Kilomita 3,500 zuwa 4,000 kuma a yayin wannan doguwar tafiya ne, matayen suke tara kwayayensu , su kuma mazajen suke samun ruwan maniyyi. To suna isa wajen sai matan su fitar da kwayayen kimanin 3,000 zuwa 5000, su kuma mazajen sai su kyankyashe kwayayen.

Babu shakka wadannan kifaye suna fuskantar hadari irin na mutuwa a yayin tafiyarsu da kuma lokacin kyankyashe kwayayen nasu.Na farko dai su matayen dake fitar da kwai sukan gaji, kayoyin jikinsu sukan fita, kuma fatar jikinsu tana komawa baka. To haka ma yake faruwa da mazajensu, nan da nan sai aga kogi yana yawo da matattunsu, amma duk da haka ba’a taba samun wani dangi na wadannan kifaye da suka ce sun gaji , baza su yi wannan aiki ba. A hakan dai wani dangi zasu taso suma su sha irin wannan wahalar kuma su kyankyashe kwayayen nasu.

Yadda kifayen Salmon suke kammala wannan hijira tasu, da yadda suke komawa cikin tekunsu bayan sun yi kyankyasa a kogi, da kuma yadda suke gane hanyarsu ta komawa din, tambayoyi ne da har yau ake bukatar amsarsu. Ko da yake dai akwai zace-zace da dama , amma dai har yau babu wata tartibiyar amsa akan haka.

Muhimmin batu anan shine, wane irin iko ne yake tafiyar da kifayen Salmon,kuma ya dawo dasu daga tafiyar dubban kilomita zuwa wurin da basu sani ba? Hakika ko shakka babu akwai wani madaukakin iko da yake juya rayayyun halittu. Shine Allah mahalicci, madaukaki kuma majibincin dukkan duniyoyi.

 • Kwanan wata 02.08.2007
 • Mawallafi Abba Bashir
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvUm
 • Kwanan wata 02.08.2007
 • Mawallafi Abba Bashir
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvUm