Hayatou ya sha kaye a zaben Hukumar CAF | Labarai | DW | 16.03.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hayatou ya sha kaye a zaben Hukumar CAF

Ahmad Ahmad dan shekaru 57 daga Madagaska ya maye gurbin Hayatou a Hukumar kwallon kafar ta Afirka CAF bayan shekaru 29 na mulkin dan kasar Kamaru.

Hukumar kwallon kafa ta Afirka (CAF) ta zabi Ahmad Ahmad dan Madagaska a wannan rana ta Alhamis inda zai maye gurbin  Issa Hayatou da ya  dauki lokaci mai tsawo ya na jan ragama ta Hukumar  CAF, abin da ke zuwa bayan zabe a taron kungiyar a kasar Habasha.Ahmad dan shekaru 57 da ke zama tsohon ministan gwamnati wanda kuma ke amfani da suna guda daya tilo ya samu nasara da kuri'u 34 da 20 a zaben shugaban na Hukumar CAF abin da ya kawo karshen shugabanci na shekaru 29 da  Hayatou dan asalin kasar Kamaru  ya kwashe ya na jan ragama ta  mulkin wannan hukuma.