Hawaii: An nemi gafara kan sakonnin hari
January 14, 2018Talla
Wani jami'in hukumar gaggawa ne ya danna madannin da bai shi yakamata a danna ba bisa kuskure, abinda ya haifar da kadawar kararrwa a wayoyin mutanen jihar cewa, " A nemi mafaka a cikin gaggawa". Sakon gaggawa ya haifar da tashin hankali ga mazauna jihar.
sai dai Vern Miyagi wani babban jami'i a hukumar gaggawa ta jihar Hawaii, ya ce "Tabbas abin da ya faru babban kuskure ne ba ganganci ba wanda ya aikata ya yi nadama. Muna ba wa al'umma hakuri, amma wannan kuskuren ba ya nufin a shagala a duk lokacin da za a aike da sanonnin gaggawa na kar-ta kwana."