1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hauhawar tsamari a kan iyakar Turkiya da Iraƙi

June 10, 2007
https://p.dw.com/p/BuJP
Tashe tashen hankula sun yi tsamari a yankin kudu maso gabashin kasar Turkiya bayan wani bam da aka dana a gefen hanya ya halaka sojoji 3 a birnin Sirnak. Jami´an Turkiya sun zargi ´yan tawayen Kurdawa da kai wannan hari. Hakan ya faru ne sa´o´i kalilan bayan da jami´an Iraqi suka zargi dakarun Turkiya da kai farmaki na tsallaken iyaka a arewacin Iraqi wanda ya janyo barna mai yawa. A halin da ake ciki ma´aikatar harkokin wajen Iraqi ta nuna rashin jin dadinta a hukumance ga jakadan Turkiya a birnin Bagadaza. A cikin makonnin baya bayan nan Turkiya ta girke karin dakaru akan iyakar ta da Iraqi yayin da shugabannin kasar ta Turkiya ke tattaunawa game da fatattakar ´yan awaren Kurdawa a tsallaken iyakar. Gwamnati a birnin Ankara ta musanta zargin da aka yi cewa dakarunta sun kutsa cikin Iraqi.