1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hauhawar kashe-kashen sojoji a Afghanistan

November 14, 2010

Hare-haren ƙunar bakin wake sun ritsa da wasu dakarun ƙawance na NATO a Afghanistan.

https://p.dw.com/p/Q8R7
Hoto: AP

Aƙalla sojojin ƙawance biyar da ke aikin ƙarƙashin ƙungiyar tsaro ta NATO sun rasa rayukansu sanadiyar tashin bama-bamai da aka fiskanta a Afghnistan. Wata sanarwa da rundunar ISAF da ke aiki ƙarƙashin kulawar NATO ta fitar ta nunar da cewa biyu daga cikin sojojin sun gama da ajalisinsu a lokacin tarwatsewar bama-bamai a kudacin ƙasar. yayin da harin ƙunar bakin wake da masu tsaninin kishin addini suka ƙaddamar a gabashin Afghnistan ya ritsa da biyu da cikin dakarun.

Waɗannan hare-haren sun zo ne mako guda kafin gudanar da taron birnin Lisbonne da ƙungiyar tsaro ta NATO za ta yi amfani da shi wajen duba irin ci gaba ko akasin haka da aka samu a yaƙi da ta'adi a ƙasar Afghanistan. 2010 dai, ita ce shekarar da sojojin ƙawance suka fi rasa rayukansu a Afghanistan tun bayan ƙaddamar da yaƙi da ta'adi a wannan ƙasa a aka yi shekaru taran da suka gabata. Dakaru 642 ne suka rigamu gidan gaskiya a cikin wannan shekara a Afghanistan, ciki kuwa har da Amirkawa 440.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Umaru Aliyu