1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

hauhauwar ƙamari tsakanin Koreya da Korea

June 15, 2010

Korea ta arewa ta yi barazanar kai wa takwararta ta kudu hari idan MDD ta zargeta da ruruta wutan rikincin da ke tsakaninsu.

https://p.dw.com/p/Nrfh
Makamin da Koreya ke niyar amfani da shiHoto: AP

Korea ta arewa ta gargaɗi Majalisar Ɗinkin Duniya da ta guji ɗora mata alhakin rikicin da ke tsakaninta da takwarta ta kudu. Jakadan Koreyar ta arewa a majalisar Ɗinkin Duniya ya ce idan kwamitin sulhu ya zargi ƙasarsa ta laifin nitsar da jirgin ruwa da ya haifar da taƙaddama tsakaninsu, to lalai za ta kai ma Koreya ta kudu hari. koreya ta arewan na nema MDD ta bata damar ganin inda haɗarin da ake zarginta da haddasawa ya faru.

Komitin sulhu na Majalisar ta Ɗinkin Duniya ta bukaci ƙasashen biyu wato Koreya ta kudu da kuma ta arewa da su guji ɗaukar duk wani mataki da zai haifar da sa in sa tsakaninsu. Tun watanni ukun da suka gabata ne, Koreya ta kudu ta zargin takwararta ta arewa da nintsar mata da jirgin ruwan, da kuma ya haddasa salwantar rayukan wasu sojojinta na ruwa.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

 Edita: Ahmed Tijjani Lawal