Hattara a game da wariyar Jinsi a Jamus | Labarai | DW | 07.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hattara a game da wariyar Jinsi a Jamus

Wasu ƙungiyoyin kare hakkin bil Adama sun gabatar da jerin shawarwari ga baƙi musamman bakabaken fata wadanda za su zo kallon ƙwallon ƙafa a Jamus, da su yi hattara domin gujewa faɗawa tarkon yan nuna wariyar jinsi. A saƙon da ƙungiyar ta yaɗa ta yanar Gizo, ta baiyana cewa a zahiri ana kai hare hare a kan baƙi baƙaƙen fata musamman a gabashin Jamus da kuma wasu yankuna a gabashin birnin Berlin, a saboda haka ta shawarci maziyar ta masu shaáwar kallon ƙwallon ƙafa su kasance tare da wayar hannu ta salula domin tuntubar yan sanda don kare lafiyar su. An jima ana tafka muhawara a yan makwannin da suka gabata a game da batun ko ƙasar Jamsu na fuskantar ƙaruwar aƙidar nuna wariyar jinsi musamman a gabashin ƙasar wanda hakan ka iya dakushe martabar ta a idanun duniya.