Hatsarin jirgin sama a Iran | Labarai | DW | 06.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hatsarin jirgin sama a Iran

Wani karamin jirgin sojin kasar iran kirar C130 yayi hatsari a dazu dazun nan, bayan ya tokari wani gida mai hawa goma a cikin birnin Tehran.

Rahotanni dai daga kasar a yanzu haka na nuni da cewa mutane kusan 126 ke cikin jirgin a lokacin da wannan hatsari ya faru.

Ya zuwa yanzu dai an nunar da cewa mutane 94 ne suka rasa rayukan su wasu kuma da dama suka jikkata.

Bayanai dai sun shaidar da cewa hatsarin wanda ya faru a lokacin da jirgin ke kann hanyar sa ta zuwa filin jirgin saman Bandar Abbas daga filin jirgin saman Mehrabad, yayi wannan karon ne bayan daya fuskanci wasu yan matsaaloli dake da nasaba da injin jirgin.

Rahotanni dai a yanzu haka na nuni da cewa ma´aikatan bayar da agajin gaggawa na kasar na can naci gaba da aikin su na ceto a gurin da wannan abu ya faru.