1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hatsarin jirgin ruwa ya rusta da ɗaruruwan baƙin haure

April 4, 2009

Jaridun Jamus sun mayar da hankali kan wannan hatsarin wanda ya auku a gaɓar tekun ƙasar Libya

https://p.dw.com/p/HQHh
Baƙin haure daga Afirka dake shiga Italiya ta ruwaHoto: AP

Baƙin hauren Afirka/Ivory Coast/Afirka Ta Kudu

Ko da yake a wannan makon mai ƙarewa duniyar gaba ki ɗaya ta karkata ne a birnin London inda aka gudanar da taron ƙolin ƙasashen ƙungiyar G20 masu ƙarfin tattalin arziki a duniya, to amma wasu jaridun Jamus sun mayar da hankali kan muhimman abubuwan da suka faru a nahiyar mu ta Afirka musamman dangane da hatsarin jiragen ruwan nan ɗauke da ɗaruruwan baƙin haure daga wannan nahiya. A rahoton da ta buga jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta fara da cewa.

Flüchtlinge aus Libyen
Baƙin haure daga AfirkaHoto: AP

"Wasu ƙananan jiragen ruwa uku da kowanensu ya ɗauke mutane kimanin 300 sun nitse a gaɓar tekun ƙasar Libya, kuma har zuwa ranar Talata wato ranar da aka dakatar da aikin ceto, ba a ga mutane sama da 200 ba. Ta ce ɗaukacin baƙin hauren ´yan ƙasashen Afirka kudu da Hamada ne sai kuma ´yan ƙasashen Tunisia da Masar. A cikin shekarun baya-bayan yawan baƙin haure dake bi ta Libya a ƙoƙarin su na shigowa Turai ya ƙaru matuƙa yayin da hukumomin ƙasar ke yin biris da wannan matsala da cewa ta nahiyar Turai ce. Jaridar ta ce fata a nan shi ne za a rage yawan masu bi ta wannan hanya ma haɗari idan yarjejeniyar haɗin guiwar kan tsaron iyaka tsakanin Libya da Italiya ta fara aiki a ranar 15 ga watan Mayu."

Ita kuwa a sharhinta jaridar Tageszeitung cewa ta yi:

"Yayin da a nan Turai ake mamakin yadda baƙin hauren ke sadaukar da rayukansu don su shigo Turai, su kuwa baƙin hauren na ganin kansu a matsayin jarumai waɗanda ke ƙauracewa wahalhalun da nahiyar ke ciki. To sai dai ɗaukacinsu ba ´ya´yan talakawa ba ne musamman bisa la´akari da maƙudan kuɗaɗen da suke biya kafin a tsallaka da su zuwa Turai. Ta ce daga cikinsu akwai ma´aikatan jiya da ƙwararrun ma´aikatan da ´yan kasuwa waɗanda nahiyar ta Afirka ke matuƙar buƙatarsu to amma ba sa iya jurewa matsalolin da wannan nahiya ke ciki."

WM 2006 Argentinien Elfenbeinküste Didier Drogba
Didier Drogba kaftan ɗin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Ivory CoastHoto: AP

Daga matsalar baƙin hauren yanzu sai kuma wani bala´i da ya auku a ƙasar Ivory Coast wato Kodivuwa lokacin wasan ƙwallon ƙafa tsakanin ƙasar da Malawi. A rahoton da ta buga jaridar Tagesspiegel cewa ta yi:

Ivory Coast

"A lokacin da magoya bayan ´yan wasan ƙwallon ƙafa na Ivory Coast ke kashe kwarkwatan ido a wasan ƙwallon ƙafa ba su san wasu ´yan ƙasar su aƙalla 22 sun rasu a tsakaninsu ba sai daga baya. Hakan dai ya auku ne sakamakon turmutsitsi a wajen filin wasan dake a birnin Abidjan. Jaridar ta rawaito cewa ´yan kallo sama da dubu 50 shiga filin wasan maimakon dubu 35. Sannan wasu rahotannin sun ce an sayar da tikiti sama da dubu 200 a bayan fage. An zargi hukumomin tsaron ƙasar da amfani da hayaƙi mai sa hawaye don tarwatsa jama´a da suka yi dafifi a wajen filin wasan. Saboda haka wasu jaridun ƙasar suka bayyana nasarar lashe wasan da ƙasar ta yi da cewa nasara ce ta zubar da jini."

Afirka Ta Kudu

Südafrika Jacob Zuma vor Gericht
Shugaban ANC Jacob ZumaHoto: AP

"Aski ya kai gaban goshi a yaƙin neman zaɓe a Afirka Ta kudu inji jaridar Neues Deutschland tana mai nuni da zaɓen shugaban ƙasa da zai gudana a ranar 22 ga watannan na Afrilu inda ta ce ba shakka jam´iyar ANC ce zata lashe zaɓen. Ko da yake har yanzu ana cece-kuce game da batun cin hanci da akan shugaban ANC kuma mutumin da ake kyautata zato zai lashe zaɓe wato Jacob Zuma, amma bisa ga dukkan alamu hakan ba zai yi wani tasiri na a zo a gani ga sakamakon zaɓen ba."

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Hauwa Abubakar Ajeje