Hatsarin dusar kankara ya halaka mutane a Jamus | Labarai | DW | 02.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hatsarin dusar kankara ya halaka mutane a Jamus

Wani rufin zauren wasanni kann kankara a garin Bad Reichenhall dake jihar Beberia a nan Jamus ya fado kasa a dai dai lokacin da ake kyautata zaton mutane kusan hamsin na ciki.

Ya zuwa yanzu dai an shaidar da rasuwar mutane uku ciki har da yaro guda wasu mutane ashirin kuma sun jikkata.

Ana kuma kyautata zaton cewa a nan gaba kadan yawan mutanen da suka rasu ko kuma jikkatar ka iya karuwa.

Kawo yanzu dai babu tabbataccen labarin musabbabin faruwar wannan al´amari.

Duk kuwa da dusar kankara dake ci gaba da zuba a garin, jami´an bayar da agajin gaggawa naci gaba da gudanar da aiyukan su.