Hasashen bullar cutar murar tsuntsaye a Habasha | Labarai | DW | 28.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hasashen bullar cutar murar tsuntsaye a Habasha

Mahukunta a kasar Habasha sun sanar da fara gudanar da gwaji akan wasu dubbannin tsuntsaye dake da jibinta da kaji da suka rasu.

Daukar wannan matakin kuwa ya samo asaline a kokarin da mahukuntan kasar keyi na sanin ko hakan nada nasaba da cutar nan ta murar tsuntsaye mai nau´´in H5N1, ko muma a´a.

Rahotanni dai sun nunar da cewa mahukuntan kasar sun aike da wani sanfuri daga cikin gwaji da aka gudanar akan tsuntsaye sama da dubu shida, izuwa kasarr Italiya don tantance wannan zargi da ake .

Ya zuwa yanzu dai bayanai sun tabbatar da cewa kasar ta Habasha da ragowar kasashen gabashin Africa irin su Kenya da Tanzania da kuma Uganda ka iya fuskantar bullar wannan cuta a kasashen nasu bisa la´akari da irin shigi da fici na tsuntsayen daji masu hijira daga wannan kasa izuwa wannan, ko kuma daga wannan nahiya izuwa waccan nahiya.