Hasashe game da tattalin arzikin Jamus | Siyasa | DW | 30.07.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Hasashe game da tattalin arzikin Jamus

Alƙaluman tattalin arzikin sun hango cewar Jamus zata samu koma baya na kashi 6,4 cikin ɗari a wannan shekara.

default

Hukumar ƙiddidigar tattalin arzikin Jamus( DIW)

Ba zato ba tsammani al'amuran tattalin arziƙin duniya sun fara farfaɗowa sannu a hankali. A nan Jamus kamfanoni na samun ƙarin kwangila a yayin da China ke samun bunƙasar yawan abubuwan da kamfanoninta ke samarwa, sannan a Amurka kuma 'yan kasuwa sun fara samun ƙwarin guiwa bisa manufa. To sai dai kuma bisa ga ra'ayin manazarta al'amuran tattalin arziƙi a cibiyar binciken tattalin arziƙin Jamus dake Berlin, ba za a samu bunƙasa a cikin gaggawa ba.

Cibiyar binciken tattalin arziƙin Jamus dake birnin Berlin tana batu ne a game da daidaituwar al'amuran tattalin arziƙi a maimakon bunƙasa. Domin kwa ko da yake a ƙasashe da dama, kamar dai Amurka da China an fara samun sararawa, amma fa har yau ba a hangen wata bunƙasa. Jamus zata samun koma-bayan tattalin arziƙinta da misalin kashi 6.4% a wannan shekarar, kuma a shekara mai zuwa ƙasar ba zata samu wata bunƙasa ta a zo a gani ba, inda aka yi hasashen bunƙasar kashi 0.5%. Bisa ta bakin Christian Dreger, shugaban sashen kula da daidaituwar al'amuran tattalin arziƙi a cibiyar binciken tattalin arzƙin Jamus dake Berlin, ƙasar zata daɗe tana fama da raɗaɗin koma bayan tattalin arzƙinta.Ya ce: Jamus ta dogara ne kacokam akan bunƙasar tattalin arziƙin duniya domin ƙaruwar yawan kayayyakin da take fitarwa zuwa ƙetare. Amma a halin yanzu ƙasar na gudanar da cinikinta ne a ƙasashen da suke farfaɗowa daga koma bayan tattalin arziƙin duniya sannu a hankali. Muhimmin abu ga Jamus shi ne halin da ake ciki a yankunan tsakiya-maso-gabacin Turai. Sannu a hankali ne ƙasashen yankin ke farfaɗowa, lamarin dake haifar da tafiyar hawainiya ga cinikin ketare na Jamus.

Wani abu mai muhimmanci ga cinikin ƙetare na Jamus kuma shi ne ka da a wayi gari matakan kariyar ciniki sun zama ruwan dare tsakanin ƙasashe. Fuskantar irin wannan hali zai sake mayar da hannun agogo baya dangane da ci gaban da ake samu a yanzu. Wai abin lura game da matsalar koma bayan tattalin arziƙin shi ne kawo yanzu bata rutsa da kasuwa ƙodago ba. Cibiyar binciken tattalin ariƙin ta Jamus dake Berlin tayi hasashen cewar a shekara mai zuwa yawan marasa aikin yi aƙasar ba zai zarce mutum miliyan 4 da dubu ɗari bakwai ba, kuma galibi matsalar zata fi shafar kamfanonin sarrafa ƙarafa ne da motoci. Dangane da cinikin ɗaiɗaikun mutane kuwa al'amura na tafiya salin-alin saboda mutane na ci gaba da sayayya duk da koma bayan tattalin arziƙin ƙasar. To ko daga ina waɗannan kuɗaɗe ke fitowa. Stefan Kooths daga cibiyar binciken tattalin arziƙin yayi bayani akan haka yana mai cewar:

Ya ce:Dalilin haka shi ne kasancewar matsalar bata rutsa da kasuwar ƙodago ba, ta yadda mutane ke cin gajiyar wannan daidaituwa da aka samu. Kuma dangane da shawarar da gwamnati ta tsayar na bunƙasa yawan kuɗaɗen fansho tun daga shekara mai zuwa yawan kuɗaɗen shiga zai ƙaru ga jama'a ta yadda a nasu ɓangaren ba zasu yi fargabar kashe kuɗi ba.

Mawallafi: Braden,Benjamin/ Lawal

Edita: Awal