Harkokin zabe a kasar Venezuela | Labarai | DW | 03.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harkokin zabe a kasar Venezuela

Miliyoyin mutane da suka can can ci yin zabe a kasar Venezuela na ci gaba da kada kuri´un su, don zabar shugaban kasa.

Shugaba Hugu Chavez, wanda ke adawa da Amurka, kuma daya daga cikin yan takarar, a yanzu haka akwai kyakkyawan zaton cewa shine zai lashe zaben, don sake wa´adi na shekaru shida a madafun ikon kasar.

Rahotanni dai sun rawaito mai adawa dashi, wato Mr Manuel Rosales na cin alwashin samun nasarar wannan zabe, akan abokin karawar tasa, daya soka a matsayin mai mulkin gurguzu irin na kasar Cuba.

Bayanai dai sun shaidar da cewa Mr Rosales, na da ra´ayi ne na daidai ta harkokin kasuwa a kasar , idan ya dare madafun ikon.

Shi kuwa Hugu Chavez, mutum ne dake da karbuwa a tsakanin talakawa da kuma ma´aikata a kasar, wadanda ke goyon bayan shirin sa na kawar da talauci.