Harkokin tsaro sun inganta a Ivory Coast bayan harin jiya litinin | Labarai | DW | 03.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harkokin tsaro sun inganta a Ivory Coast bayan harin jiya litinin

Dakarun sojin gwamnatin Ivory Coast sun samu galabar dakile fitinar da wasu yan bindiga dadi a kasar suka tayar a birnin Abijan a jiya litinin.

Kafin dai shawo kann wannan al´amari bayanai sun nunar da cewa mutane a kalla goma 13 ne suka rasa rayukan su, ban da wasu da suka jikkata.

Wannan rikici dai ya samo asali ne bayan da yan bindiga dadin dake son tada zaune tsaye suka kai hari a wasu barikin sojin kasar biyu dake birnin na Abijan.

A cewar kakakin sojin kasar, Babri Gohourou, daga cikin wadanda suka rasa rayukan nasu akwai soji uku dake marawa yan tawayen baya da kuma mutane goma da suka kawo harin.

Ba a da bayan haka, dakarun sojin kasar sun kuma samu galabar cafke mutane 32 dake da hannu a cikin kawo wannan hari, dake a matsayin babban kalubalen dorewar sabuwar gwamnatin da aka kafa kwana kwa nan nan a karkashin faraminista Charles Konnen Banny.