1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

HARKOKIN TSARO A KASAR SAUDI ARABIA:

JAMILU SANINovember 11, 2003
https://p.dw.com/p/Bvnh
A kasar Saudi Arabai yau ne sarki fahad ya bada gargadin cewa mahukuntan na Saudia zasu sanya kafar wando daya da dukanin yan kungiyoyin tsagerun musulmin kasar,hakan ne ma ya sanya gwamnatin ta saudia ta dauki matakan aika duban soji zuwa yankuna masu tsari da suka hadar da birnen Makkah da madina,don kare lafiyar mahajata da suka ziyarci kasar don gudanar da aiyukan su na Ibada cikin wanan wata mai alfarma na Ramadan.

Tun bayan harin bomb din da yayi sanadiyar mutuwar mutane 17 a birnin Riyadh a karshen mako ne ya sanya,sarki Fahd ya bada gargadin cewa gwamnatin saudi zata dauki matakan da suka dace ma yaki da yan ta'ada dake kai hare hare na ta'adanci a kasar ta saudia.

Da yake jawabin ga yan majalisar masarautar Saudia da aka saba gudanarwa mako mako,sarki Fahd ya baiyana cewa za'a tanadi hukunci mai tsananin gaske kann dukan mutumin da aka samu da hanun na barazana ga harkokin tsaron saudia da kuma yan kasar harma da baki dake zaune a kasar baki daya.

Majiyar tsaron saudia ta shaidawa kamfanin dilancin labaru na AFP cewa,a halin yanzu an jami'an tsaro da suka hadar da soji da yan sanda 5,000 zuwa birnin Makkah,inda aka baiyana cewa alumar muslmi daga kasahen duniya miliyan biyu da dubu dari biyar suka issa birnin Makkah don gudanar da aiyukan su na ibada a kwani goman da suka rage na watan Ramadan mai alfarma. Majiyar tsaron dai ta saudia ta kara da cewa an kara tsaurara matakan tsaro ne,tun bayan da aka sami wasu bayanai dake nuna cewa yan kungiyar al-Qaeda na shirin kai hari birnin Makka. Haka zalika an baiyana cewa za'a kara samar da jami'an tsaro masu yawan gaske a birnin Medina,birni na biyu mafi tsarki a kasar ta Saudi Arabia.

Mukadashin ministan dake lura da aiyukan hajji Hatem Qadi yau talata ya shaidawa jaridar Al-Hayat ta Saudia cewa duk kuwa da wanan hali da ake ciki,har kawo yanzu alumar musulmi daga kasahe dabam dabam na duniya na cigaba da zuwa wanan kasa.

Birnin dai na Makkah na zaman daya daga cikin yankuna da aka yi dauki ba dadi tsakanin jami'an tsaron saudia da kuma yan bindiga dadi na kungiyar al-Qaeda.

Mahukuntan dai na Saudia sun baiyana cewa a ranar uku ga wanan wata ne dai suka murkushe,yunkurin da aka yi na kaiwa Alhazai hari a birnin Makkah birni mafi tsarki a duniya baki daya.

A tsakiyar watan Yunin da ya gabata,jami'an tsaron saudia sun kai farmaki wata maboya ta yan kungiyar al-Qaeda dake birnin na Makkah,inda har ma suka sami nasarar kashe mutane biyar tare kuma da kame 12 daga cikin yan kungiyar ta al-Qaeda.

Sarki Fahd ya mika ta'aziyarsa ga iyalan wadanda suka rasa yan uwan su,cikin hadarin bomb din da ya faru a birnin Riyadh karshen mako.

A yanzu haka dai manyan maluman Saudia na nan na shirin samar da masalaha ta sulhu tsakanin gwamnatin ta saudia da matasan kasar dake neman a samar da sabon sauyi na gwamnati a kasar ta Saudia.