1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harkokin siyasa na ci gaba da zafafa a Venezuela

Ibrahim SaniDecember 1, 2007
https://p.dw.com/p/CVWf

A gobe ne za a gudanar da zaɓen raba gardama a Venezuela, dangane da gyaran fuska ga kundin tsarin mulkin ƙasar. Batun wa´adi na shugaban ƙasa da kuma rage cikakken ikon shugaban babban bankin ƙasar na daga cikin abubuwan da za a yiwa kwaskwarima. Ma su nazarin siyasa na kallon matakin ne, a matsayin wata kafa da ka iya bawa shugaba Hugu Chavez dama ce na yin tazarce a karo na uku a jere. Kafafen yaɗa labarai sun rawaito Mr Chavez na gargadin Amirka da daina katsalandan, a harkokin siyasa a ƙasar. Goyon bayan da Amirka ke ba wa ´Yan adawa a cewar Mr Chavez, abune da ka iya gurgunta zaɓen na gobe lahadi.