Harkokin siyasa a Zambia sun fara kan kama | Labarai | DW | 01.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harkokin siyasa a Zambia sun fara kan kama

Jam´iyyun adawa uku na kasar Zambia sun cimma yarjejeniyar fitar da dan takara daya da zai kalubalanci shugaba Levy Mwanawasa a zaben shugaban kasa da ake shirin gudanarwa.

A cewar mai magana da yawun jam´iyyun hadin gwiwar na UDA, jam´iyyar tasu zata gudanar da babban taro a nan gaba kadan don zaben mutumin da zai musu wannan takara.

Daukar wannan mataki dai a cewar kakakin jam´iyyar ta UDA, yazo ne a bisa muradin yan kasar na fitar da mutumin dai zai fafata da shugaba mai ci a neman wannan mukami.

Masu nazarin siyasa dai na kallon wannan mataki a matsayin wata kafa da shugaba Mwanasawa zai fuskanci babban kalubale a kokarin da yake na yin tazarce a gadon mulkin kasar a karo na biyu.

Rahotanni dai sun tabbatar da cewa babu wata tsayayyiyar rana ta gudanar da wannan zabe, to amma bayanai sun nunar da cewa watakila ya kasance a karshen wannan shekara da muke ciki.