Harkokin siyasa a Pakistan | Labarai | DW | 22.11.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harkokin siyasa a Pakistan

Jam´iyyun adawa a Pakistan na ci gaba da adawa da hukuncin kotun ƙolin ƙasar, a game da yarjewa Mr Musharraf yin takara. Yin hakan a cewar Jam´iyyun ya yi karan tsaye ga dokokin ƙasar. Da ranar yau ne Sabbin Alƙalan da aka naɗa a kotun ƙolin ƙasar su ka yi watsi da ƙarar dake ƙalubalantar takarar shugaba Musharraf. Ƙarar a cewar rahotanni na a matsayin ta ƙarshe, a jerin ƙararrakin da ´Yan adawa su ka shigar ne, don ƙalubalantar takarar ta Mr Musharraf. Hukuncin na baya-bayan nan a yanzu haka, zai bawa Mr Musharraf dama na yin ta zarce a karo na biyu a jere na tsawon shekaru biyar. Mr Musharraf a baya ya ce da zarar kotun ƙolin ta yarje yin tazarcen to zai ajiye kakinsa, tare da zamowa cikakken shugaban ƙasa na farar hula. Jam´iyyun adawa na ƙasar na ci gaba da adawa da hukuncin kotun ƙolin tare da kiran da a ƙauracewa zaɓen na gama gari. An shirya gudanar da zaɓen ne, a ranar 8 ga watan Janairun sabuwar shekara ta 2008.