1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harkokin siyasa a kasar Masar

ibrahim saniSeptember 27, 2005

Fadi tashin harkokin siyasa a kasar Masar bayan rantsar da shugaba Hosni Mubarak a matsayin ta zarce a karo na biyar a jere.

https://p.dw.com/p/BvZN
Hoto: AP

Ya zuwa yanzu dai rahotanni sun shaidar da cewa idan shugaba Hosni Mubarak ya samu damar kammala wannan dama ta shekaru shida daya kara samu daga yan kasar to a takaice ya shafe kusan shekaru 25 ke nan yana jan ragamar mulkin kasar a jere.

Koda yake hausawa kance da kyar nasha yafi da kyar aka kamani, bayanai sun shaidar da cewa shugaba Hosni Mubarak ya samu kusan kashi tamanin da takwas daga cikin kuriun da aka kada a lokacin zaben shugaban kasar na watan satumba, duk da cewa kashi 23 na alummar kasar miliyan 32 ne kawai suka fito don kada kuriun nasu a lokacin wannan gagarumin zabe dake a matsayin irin sa na farko a tarihin kasar.

Jim kadan bayan ya karbi rantsuwa, shugaba Mubarak yayi alkawarin daukar sabbin matakai na inganta harkokin mulkin siyasa da dimokradiyya a hannu daya kuma da farfado da tattalin arzikin kasar.

Bugu da kari sabon shugaban kasar ta Masar ya kuma yi alkawarin daukar kwararan matakai na rage radadin rashin aikin yi dake damun da yawa daga cikin yan kasar.

Har ilya yau Mubarak ya tabbatarwa da mutanen kasar cewa zai yi aiki tukuru a wannan lokaci wajen ganin ya cika dukkannin alkawuran daya daukarwa alummar kasar a lokacin yakin neman zaben sa.

Mubarak wanda ya dare garakar mulkin kasar bayan dokar ta baci da aka saka jim kadan bayan kisan gillar da akayiwa shugaba Anwar Saddat a shekara ta 1981,a yanzu haka na fuskantar matsin lamba a cikin gida da kuma waje game da irin yadda al,amurra ke tafiya a kasar a siyasan ce.

A dai karshen jawabin sa Mubarak ya shaidar da cewa tsohuwar gwamnatin sa zata ci gaba da gudanar da aikinta har zuwa lokacin da za a gudanar da zaben yan majalisun dokokin kasar da ake sa ran yi a watan nuwamba na wannan shekara da muke ciki,wanda daga nan ne za a rushe ta a kuma kafa wata sabuwar gwamnatin.

Duk da cewa an gudanar da wannan biki na rantsuwa, ragowar yan takarar neman shugabancin kasar guda tara sun ci gaba da sukar sakamakon zaben daya bawa Mubarak nasara da cewa an tafka magudi da aringizon kuriu a cikin sa .

Bugu da kari da yawa daga cikin jamiyyun adawar sun kuma soki lamirin sabon matakin da aka gudanar da wannan zabe na shugaban kasa da cewa ya kaucewa tsari na mulkin dimokradiyya, ta hanyar yadda aka soke takarar wasu ba tare da wasu gamsassun dalilai ba.

Rahotanni dai sun shaidar da cewa shugaban na masar ya karbi rantsuwar ne a gaban shugaban majalisar dokokin kasar, wato Fathi serour a lokacin wani kwarya kwaryan biki da aka gudanar a babban birnin kasar wato Kairo a wani hali na tsattsauran matakan tsaro.

Ya zuwa yanzu kuma babban abin da da yawa daga cikin yan kasar suka fi mayar da hankalin su kai shine na zaben yan majalisun dokoki da ake shirin yi a watan nuwamba. Hakan kuwa ya samo asali ne da cewa a lokacin ne za a yi gumurzu mai yawan gaske bisa irin muhimmancin dake tattare da hakan musanmamma a lokacin zaman su a zauren majalisa.

Koda yake a lokacin jawabin sa , Shugaba Mubarak yayi alkawarin ganin an tabbatar da gaskiya da kuma adalci a lokacin wannan zabe na gaba amma duk da haka da yawa daga cikin jamiyyun adawar kasar na zargin yar gidan jiya za a kara yi a lokacin zaben.

Rahotanni dai sun nunar da cewa Shugaba Mohd ghaddafi na kasar Libya na daga cikin shugabannin kasashen daya halarci wannan biki na yau. Ragowar shugabannin kuma akwai jakadu na kasashe daban daban na duniya da kuma mukarraban su. Har ila yau bayanai sun shaidar da cewa, daya daga cikin yan takarar shugabancin kasar kuma babban dan adawa wato Ayman Nur, wanda yanzu haka yake gaban kuliya bisa zargin almundahanar takardu na daga cikin mutanen da suka sami damar halartar wannan biki.