HARKOKIN SIYASA A KASAR IRAQI. | Siyasa | DW | 04.02.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

HARKOKIN SIYASA A KASAR IRAQI.

yan jaridu a lokacin zaben gama gari a iraqi.

default

A yanzu haka dai bayanan da suka iso mana daga kasar ta Irak sun shaidar da cewa sakamakon zaben gama gari daya fara fitowa ya nunar a fili cewa gamayyar jamiyyu na Darikar Shai,a ne ke a kann gaba a yawan kuriu da aka kidaya.

A cewar wani babban jamii daga hukumar zaben ta iraqi,a yanzu haka jamiyyar ta yan shai,a da Ayatolla Ali Al sistani kewa jagoranci nada kashi 73 a cikin dari na kuriu miliyan daya da dubu dari shida da aka kidaya.

Bugu da kari jamiin ya kuma kara da cewa jamiyyar faraministan Iyad Alawi itace ta biyu data samu kashi 18 daga cikin dari na wan nan kididdiga da muka ambata a sama.

Wan nan dai sakamakon zabe daya fara fitowa ya hadar da kuriun mazabu a kalla guda goma ne daga cikin runfunan zabe da ake dasu.

A waje daya kuma daya daga cikin shugabannin yan shi,a na iraqin wato Moqtada Al Sadr ya bukaci da Amurka ta fito fili ta fadi lokacin da zata janye sojojin ta daga kasar ta iraqi tun da an kammala zabe.

A cewar Moqtadar Sadr lokaci yayi da kawayen Amurka zasu takura mata nata fadi lokacin da zata janye rundunar sojin ta daga kasar ta iraqi don bawa yan kasar damar mulkar mkansu da kansu.

A can baya dai Shugaban kasar ta Iraqi Ghazi Al yawar ya shaidawa duniya cewa janyerwar sojojin Amurka daga kasar a yanzu haka ka iya daukar lokaci bisa rashin kyakkyawan tsaro da ba a dashi a halin yanzu. A don haka a ganin sa har yanzu da sauran lokaci.

A kuwa dai dai lokacin da hukuma