1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harkokin siyasa a janhuriyar Benin

June 24, 2006
https://p.dw.com/p/Busg
Majalisar dokokin janhuriyar Benin dake yammacin Afirka ta kada kuri´ar yiwa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima don karawa kanta karin shekara daya na mulki. Hakan dai ya ta da hankalin kungiyoyin fafatukar shimfida sahihiyar demukiradiya a kasar, wadanda suka yi tir da wannan mataki. Daukacin wakilan majalisar dokokin sun kada kuri´ar amincewa da karin wa´adin majalisar daga shekara hudu zuwa biyar. Hakan na nufin kenan sai a shekara ta 2008 za´a gudanar da sabon zaben ´yan majalisar dokoki. Wannan matakin ya daidaita wa´adin aikin majalisar da na shugaban kasa kamar yadda yake a daukacin kasashen yammacin Afirka. Amma kungiyoyin dake kamfen din inganta harkokin zabe a Benin sun zargi ´yan majalisar da nuna son kai. A cikin watan maris aka zabi sabon shugaba Thomas Boni Yayi bayan tsarin mulki ya tilastawa tsohon shugaba Mathiew Kerekou wanda ya dade akan mulki sauka daga mukamin shugaban kasa.