Harkokin siyasa a Israela | Labarai | DW | 26.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harkokin siyasa a Israela

Sabuwar jamiyyar Faraminista Arial Sharon na Israela, wato Kadima, tace matukar an zabi Sharon a matsayin ta zarce a karo na uku a jere to babu shakka gwamnatin zata amince da kirkiro da yantacciyar kasar Palasdinu.

Bugu da kari jamiyyar ta Kadima taci gaba da cewa sabuwar gwamnatin ta Sharon za kuma tayi kokarin ganin ta sake mika wasu yankuna na kasar a hannun yankin Palasdinawa.

Wadannan kalaman dai na kunshe ne a cikin wani daftarin sabuwar jamiyyar ta Kadima data fitar a yau litinin a kokarin da take na yakin neman zabe.

Ya zuwa yanzu dai shirye shirye sun yi nisa game da gudanar da wannan zabe da aka shirya yi a ranar 28 ga watan maris na sabuwar shekara ta 2006 mai kamawa.