1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harkoki sun kankama a filayen jirgin sama a Britania

Zainab Mohd AbubakarAugust 17, 2006
https://p.dw.com/p/Bu5r

Harkoki sun fara kankama a manyan filayen saukan jiragen samna na kasar Britania,mako guda bayan jamian tsaro sun bankado shirin afkawa jirage da harin boma bomai.To sai har yanzu jamian yan sanda na cigaba da tsare yara matasa musulmi gudfa 23 da suka cafke,bisa ga amincewan Alkali,bayan zaman shariar sirri da aka gudanar jiya laraba,akan cewa ana bukatar karin lokaci na gudanar da bincike akan wadanda ake zargin.Kamfanion British Airways,wadda ta soke tashin jirage sama da 1,900,a kwanaki bakwai da suka gabata,tace ayau ta soke tashin jirage guda 19 ne kachal daga filin saukan jirage na Heathrow,ayayinda a gobe baa zaton soke ko daya.Kasancewar har yanzu babu tabbacin cewa mutane 23 dake tsare nada hannu a shirin kai wadannan hare hare,yansandan na Britania sun nemi izinin kotu ,nacigaba da tsare tare da tambayan wadanda ake zargin.