1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harkar yawon bude ido ta bunkasa a Afirka ta Kudu

October 26, 2016

Afrika ta Kudu ta shiga sahun manyan wuraren yawon shakatawa a duniya tun bayan kammala gasar cin kofin duniya a 2010.

https://p.dw.com/p/2Ril9
Wandern Südafrika
Hoto: S. Stroncik

Kayayyakin al'adun gargajiya da koramu masu cike da tsintsaye da namun daji su ne mahimman abubuwan da suke daukar hankalin kimanin mutane milliyan takwas zuwa kasar ta Afirka ta Kudu, don gane wa idonsu abubuwan masu kayatarwa.

Ruwa na kwarara a gabar wata korama wadda ke kewaye da tsaunika, a wannan wurin da aka gina katafaren wurin shakatawa da ake kira De Hoop.

Wannan wuri da ke kudancin kasar ta Afrika ta Kudu ya kunshi namun daji masu kayatarwa da tsintsaye masu daukar hankalin baki masu son kashe kwarkwatar idonsu, ga kuma nau'i kan abincin gargajiya.

Wani jami'in da ke kewayawa da baki 'yan yawon bude da ake kira Dicson ya shiga jirgin ruwan da zai kewaya da bakin nasa, inda yake cewa "lalenku marhabin da zuwa De Hopp daya daga cikin wuraren bude ido da shakatawa sanannu a Afirka ta Kudu."

A cewar Williams Stephens wani da ke yi wa 'yan yawan bude ido jagora, mutane daga ko ina na tururuwar zuwa bakin wannan ruwan don shakatawa.

"Akwai abubuwan ban sha'awa a wannan wurin yawon shakatawa ciki har da wurin da za ka hau sama ka gano abubuwan da suke nesa. De Hopp fitaccen wuri ne a Afirka ta Kudu da yake da namun daji masu kayatarwa."

Kap der der Guten Hoffnung Natur Reservat De Hoop
Yankin shakatawa na De Hoop a Afirka ta KuduHoto: picture-alliance/dpa/R. Fuchs

Ko a cikin watannin Yuni da Oktoba wannan wuri na cigaba da kasancewa a yanayi mai ban sha'awa. Za ka iya yawo a kafarka cikin yashi har zuwa cikin ruwa, kamar yadda wani mai suna Partrick ya yi bayani.

"Baya ga yawon bude ido, ga masu sha'awar tsintsaye akwai su iri-iri, mutum yana da zabin ya dauki hayar keke don ya zagaya da kansa ya gane wa idonsa abubuwa masu kayatarwa, wasu lokutan ma za ka iya cin karo da kananan dabbobi lokacin da kake zagayawa."

A baya dai wannan gandun daji na De Hopp gonaki ne, kafin daga bisani aka maida shi wani kasaitaccen gandun dajin shakatawa da yawon bude ido, kuma har yanzu akwai gidaje da aka maida su yadda za su kayatar kuma a lokaci guda wuraren kwana. Al'ummar da ke yankin su ne ke lura da su a matsayin wata hanya ta aikin yi, saboda haka De Hopp ba wai wuri na shakatawa kadai ba, wuri ne da mutum zai karu sosai a cewar Williams Stephen.

"A bayyane take mu ne kan gaba wajen samar da ayyukan yi a wannan yankin, kuma muna horas da su hanyoyin da za su gudanar da aikinsu yadda ya kamata."

Masu ziyartar gandun dajin De Hopp don shakatawa da gane wa idonsu ababen kayatarwa na yabawa da yadda aka tsara wurin a ko yaushe.