HARIN YAN TADDA WA JIRAGEN RASHA BIYU DA SUKA FADI. | Siyasa | DW | 27.08.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

HARIN YAN TADDA WA JIRAGEN RASHA BIYU DA SUKA FADI.

An tsinci burbushin makamai da aka kaiwa jiragen Rasha hari dasu a daya daga cikin jiragen.

Faduwar Jirgin sama.

Faduwar Jirgin sama.

Jamiai sun tabbatar dacewa jiragen Rasha biyu da sukayi hadari alokaci guda ,harin yan taadda ne,domin an gano an gano abunda ya rage daga boma boman da suka dasa daga sauran burbudin jirgin,ayayinda wani sako ta yanar gizo gizo daga wata kungiyar tsageru,ta dauki alhakin kai wannan hari saboda tsoma bakin Rasha,wajen yakan yan tawayen Checchiniya.

Duk dacewa wannan na mai zama babbar barazana ga harkokin sufurin sama dage zirga zirga a wannan kasa,hukumomin na Rasha basu bada wani Umurni na dakatar da ayyukan jiragen saman kasar ba ,kamar yadda Amurka tayi bayan harin kunar bakin wake da akayi mata na 11 ga watan Satumba.

Wadannan jirage biyu dake dauke da mutane 90,sun fado a lokaci guda a ranar talata da dare.Duk da zargi da akeyi na cewa jiragen biyu sun fado ne kwanaki biyar kachal kafin a gudanar da zaben Checchiniya da yan tawayen kasar ke adawa dashi,jamian Rashan na binciken musabbabin wannan hadari,inda suke zargin gurbataccen mai,ko kuma matsala abangaren maaikatan jiragen.

Sai dai kuma kakakin hukumar tsaro ta tarayyar kasar ,Sergei Ignatchenko,yace binciken sharan bage da suka gudanar na nuni dacewa ,akalla harin kunar bakin wake aka kaiwa daya daga cikin jiragen,idan ba biyun ba.

Burbudin kayayyakin da akayi amfani dasu wa jirgin TU-154 wanda ke dauke da mutane 46,jamiai sunce miyagun makamai ne ,irin wadanda akayi amfani dasu wajen kai hare hare a gidaje a rasha a shekarata 1999,wanda ya kashe mutane 300,harin da aka danganta da yan tawayen na Checchiniya.Amma ya zuwa yanzu babu sakamakon abunda ya haddasa faduwan daya jirgin Tu-134,dauke da mutane 44,km 200 kudancin birnin Moscow.

Wata sanarwa data fito yau ta hanyar sadarwa ta yanar gizo gizo ,ta bayyana wata kungiya mai suna islambouli Brigades da rataya alhakin kaiwa jiragen biyu hari alokaci guda.To sai dai babu tabbaci dangane da wannan bayani.Bugu da kari hukumar tsaron kasar taki cewa komai dangane da hakan.

Jamian Rashan dai sun sha zargin cewa kungiyar yan tawaye dake yakan dakarun Rasha a Checchiniya na tsawon shekaru 5 da suka gabata,na samu tallafi ne daga kungiyoyin yan ta kife na kasashen waje,wadanda suka hadarda kungiyar Alqaeda.To sai dai sanarwar ta yau bata ambaci Alqaeda ba.Sanarwar haila yau na nuni dacewa akwai yan kunar bakin waken guda biyar acikin kowane daya daga jiragen biyu.A halin yanzu dai jamian Rashan sunce suna binciken wasu mata pasinja biyu dake dauke da sunayen yan checchiniya.Ya zuwa yanzu kuwa ,babu yanuwansu da suka tuntubi hukumomi dangane da wannan hadari.A baya dai mata yan kunar bakin wake sun sha kai hare hare a Rasha,wadanda ke fitowa daga Chechiniya.

Zainab Mohammed.