Harin yan bindiga dadi a bagadaza | Labarai | DW | 09.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin yan bindiga dadi a bagadaza

Mutane da dama suka rigamu gidan gaskiya ,alokacinda wasu yan bindiga dadi sukayi ta ta bude wuta a gunduwar yan darikar sunni a birnin Bagadazan Iraki a yau,a wani abunda yan sanda suka bayyana da kasancewa mafi munin yanayi a wannan kasa dake cikin fargaban fadawa yakin basasa.

Wannan sabon hari dai ya auku ne a kusa da wani masallacin yan shia,a yankin dake da mafi yawan yan sunni a yammacin bagadaza,yankin da kuma harin bomb na mota ya kashe mutane 3,cikin daren jiya,baya ga gidajen da suka kone.

Jamian tsaro da yansanda dake yankin sun bayyana cewa akalla wadanda suka mutu daga harin na yau basu kasa 40 ba,wadanda kuma suka hadar da mata da yara kanana.

A unguwar Shula dake bagadazan yankin dake dauke da yan darikar shia ,wakilin kamfanin dillancin labarai na reuters ya bayyana cewamayakan sakai na Mehdi sun tare da tituna da kone konen tayoyi,tare da sanarwa jamaa kasance a gidajensu.