Harin yan adawa a India | Labarai | DW | 04.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin yan adawa a India

India

Yan adawa na kungiyar Moist sun bindige wani dan majalisar dokoki da wasu mutane guda biyar dake halartan bukin addinin Hindu a jihar Jharkhand,dake yankin gabashin kasar India a yau.Dan majalisar dokoki Sunil Mahto,ya gamu da ajalinsa ne a wannan harin da yan tawayen suka kai a kusa da kauyen Pakuria,mai tazarar km 150 kudancin birnin Ranchi,dake zama fadar gwamnatin wannan jiha.Jamian yansanda dake yankin dai sun sanar dacewa an kashe dan majalisar mai shekaru 41 da haihuwa ne, a harin da aka kai musu a yayinda suke buga kwallon,bukin gargajiya na Holi na wannan shekara.