Harin Wuerzburg da Ansbach na da hadi da 'yan jihadi
July 26, 2016Talla
Ministan harkokin cikin gida na jihar Bavaria a nan Jamus Joachim Herrmann ya bayyana a ranar Talatan nan cewa hare-haren da aka kai a makon jiya a Wuerzburg ta hanyar amfani da gatari a cikin jirgin kasa da ma wanda ya kai hari da bam a garin Ansbach a ranar Lahadi da ta gabata, hare-hare ne da ke da alaka da masu ikirarin kaifin kishin addinin Islama.
A cewar Mista Herrmann hare-haren na Wuerzburg da Ansbach ta'addanci ne da ba za a yi sakaci a kansa ba, za a sanya idanu sosai a kansa dan kare kara afkuwar hakan a nan gaba.