Harin ta´danci a opishin jikadancin Amurika da ke birnin Damaskus | Labarai | DW | 12.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin ta´danci a opishin jikadancin Amurika da ke birnin Damaskus

Kwana ɗaya rak, bayan cikwan shekaru 5 da kai hare-haren 11 ga watan Satumber a Amurika, wasu yan takife sun abkawa opishin jikadancin Amurikar, a birnin Damaskus na ƙasar Syria.

Saidai baki ɗaya, mutanen huɗu da su ka kai wannan hari, sun rasa rayuka, a yayin da ma´aikatan opishin jikadancin, suka ƙetara rijiya da baya, ba tare da samun raunuka ba.

Ministan harakokin cikin gidan Syria, Bassam Abdel Madjid, ya ce hukumomi sun fara bincike, domin tantance dukan masu hannu a cikin wannan aikin ta´adanci.

Masharahanta a kan harakokin ta´adanci ,na ɗaukar wannan hari, a matsayin aiwartawa a zahiri, kalamomin Aiman Alzawahiri, mataimakin shugaban Alqa´ida.

A jawabin da yayi , albarkacin 11 ga watan satumber, ya nunar da cewa, hare hare masu zuwa, za su kasance a kan Amurikawa dake yankin gabas ta tsakiya.