Harin ta'addanci a Indonesiya
January 14, 2016Talla
A kalla dai an sami tashin fashewar wasu boma-bamai uku a birnin na Jakarta, a inda aka shafe sa'o'i ana bata kashi tsakanin maharan da jami'an tsaron kasar.
A yayin da yake jajantawa al'ummar kasar shugaban kasar Indonesiya Joko Widodo ya yi nuni da cewar.
"Mun yi Allah wadai da wadan nan hare-haren da suka kawo barazanar lafiyar al'umma, tuni na baiwa hukumomi umarnin kamo wandan da suke da alhakin kai hare-haren. A matsayin mu na 'yan kasa bai kamata mu razana ba, ya kamata mu zauna cikin nutsuwa domin kamai zai dawo dai-dai".
Wata majiya ta bayyana cewar mayakan kungiyar IS ne suka kai harin. Inda mutane biyu suka mutu wasu mutake akalla goma suka jikkata