Harin ta′addanci a babban asibitin sojoji na Afghanistan | Labarai | DW | 08.03.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin ta'addanci a babban asibitin sojoji na Afghanistan

Wasu 'yan ta'adda sanye cikin kayan likitoci sun kai hari da safiyar wannan Laraba a asibitin sojoji na birnin Kabul.

Afghanistan Angriff auf das Militärkrankenhaus in Kabul (picture-alliance/AP Photo/M. Hossaini)

Hayaki na tashi a asibitin sojoji na birnin Kabul

Babban asibiotin sojojin ya na dauke da gadaje akalla 400 na marassa lafiya a cewar wata majiya ta gwamnatin kasar. Mai magana da yawun ofishin ministan tsaron kasar ta Afghanistan Janar Daulat Waziri, ya sanar cewa 'yan ta'adda da dama sun shiga cikin asibitin, inda ya ce an ji karan harbe-harbe sannan daga bisani aka ji karan fashewar wasu ababe masu kama da bama-bamai.

Sai dai kawo yanzu babu wani adadin wadanda suka mutu a wannan hari. Daya daga cikin Likitocin asibitin ya rubuta ta shafinsa na Facebook cewa, 'yan ta'adda sun shiga asibitinsu a taya su da addu'a.