Harin ta´adanci a India ya hallaka mutane 55
February 28, 2006Talla
A ƙasar India, wasu mutane ɗauke da makamai sun kai hari a yankin Darmagura, wanda ya hallaka mutane 55, da jikkata wasu kimanin20.
Rahotanin jami´an tsaro, sun ɗora alhakin wannan hari, ga yan tawaye, wanda shine mafi muni a tsawan shekaru 30 da su ka wuce a ƙasar.
Yan tawayen sun kai harin, da nufin rugurguza wani sansani na mutanen da ke bada goyan baya ga gwamnati.
A halin yanzu, an baza jami´an tsaro da dama domin farautar yan tawayen.
Harin ya wakana, a jajibirin ziyara da shugaban Amurika Georges Bush, zai kai a kasar India.