Harin roka a Mogadishu yayi sanadiyar mutuwar mutane biyar | Labarai | DW | 10.02.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin roka a Mogadishu yayi sanadiyar mutuwar mutane biyar

Mutane biyar sun rigamu gidan gaskiya sannan 10 sun ji raunuka a wani harin makami mai linzami da aka kai a kudancin Mogadishu babban birnin kasar Somalia. Rahotanni sun nunar da cewa da farko sai da aka harba roka akan wani otel dake arewacin birnin inda gwamnatin wucin gadi ke wani taro. A cikin makonnin da suka gabata dai tashe tashen hankula sun karu a birnin Mogadishu. A cikin watan desamba dakarun gwamnati da taimakon kasar Habasha sun fatattaki sojojin sa kai na kotunan Islama, wadanda gabanin wannan lokaci ke rike da iko tare da tabbatar da bin doka da oda a babban birnin na Somalia.