1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin kunar wake a Tel Aviv ya halaka mutum 7

April 17, 2006
https://p.dw.com/p/Bv1e

Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas yayi Allah wadai da harin kunar bakin wake da aka kai yau a birnin Tel Aviv wanda ya halaka akalla mutane 7 ciki har da wanda ya kai harin. Abbas ya baiyana harin da cewa wani aiki na ta´addanci kana kuma yayi kira ga gamaiyar kasa da kasa da ta hanzarta daukar matakan kawo karshen tabarbarewar al´amuran a wannan yanki. Ofishin shugaban na Falasdinawa ya ce harin ya sabawa ra´ayin Falasdinawa dangane da samun kasar kansu. To sai dai a nata bangaren kungyiar Hamas ta masu zazzafan ra´ayin addinin Islama ta goyi da bayan wannan hari da cewa kare kai ne daga mamayar da Isra´ila ta yiwa yankunan Falasdinawa. A halin da ake ciki kungiyar Jihadin Islami ta ce ita ta kai harin na birnin Tel Aviv.