1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin kunar bakin wake a Pakistan

Kungiyar Taliban ta yi ikirarin kai wani harin kunar bakin wake a Pakistan a cikin wata kasuwa da ke a garin Parachinar, da ke a arewa maso gabashin kasar wanda a ciki mutane 22 suka mutu kana wasu 57 suka jikkata.

Shaidun gani da ido sun ce sun ga gwarwarkin mutane kwance cikin jini,jina-jina,wannan shi ne hari irinsa na biyu mafi muni da aka kai a garin na Parachinar bayan wasu jerin hare-haren da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane 130 a cikin watan Janairun da ya gabata.