Harin kunar bakin wake a Morocco | Labarai | DW | 12.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin kunar bakin wake a Morocco

Mahukuntan ´kasar Morocco sunce wani dan kunar bakin wake ya tada bam din dake jikinsa a wani gidan internet a birnin Kasablanka a daren jiya,yana mai halaka kansa tare da raunata wasu mutane 3,yan sanda sunce suna gudanar da bincike akai.

Bam din ya tashi ne a lardin Sidi Moumen mazaunin wasu yan kunar bakin wake su 13 da suka halaka kawunansu tare da wasu 32 a 2003.