Harin kunar bakin wake a Jordan | Labarai | DW | 10.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin kunar bakin wake a Jordan

Kungiyyar Al qeda ta Usama bin Ladan dake da reshen ta a Kasar Iraqi tayi ikirarin cewa itace ta kai harin kunar bakin waken nan na birnin Amman dake Jordan .

Kungiyyar ta Alqeeda da ake mata kallon kungiyyar yan Taadda ta fadi hakan ne a cikin wata bayani data aike izuwa yanar giza gizan sadarwa na duniya wato Inter net a Turance.

Idan dai za a iya tunawa wannan hari na kunar bakin wake ya zuwa yanzu yayi sanadiyyar rasuwar mutane sama da hamsin banda wasu kuma da suka jikkata.

Jamian yan sanda na kasar sun shaidar da cewa da yawa daga cikin wadanda suka rasa rayukan nasu yan asalin kasar ta Jordan ne.