Harin kunar bakin wake a Islamabad | Labarai | DW | 26.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin kunar bakin wake a Islamabad

Mutane biyu ne suka rasa rayukansu kana wasu shida suka samu raunuka ,alokacinda wani dan kunar bakin wake ya tayar da bomb a gidan saukan baki na Marriot ,dake birnin Islamabad din kasar Pakistan.Ministan harkokin cikin gida na kasar ya sanar dacewa dankunar bakin waken da daya daga cikin masu tsaron harabar ginin ne suka rasa rayukansu a wannan harin.Marriot Hotel dai na mai kasancewa daya daga cikin manyan wuraren saukan baki,da jakadun kasashe da manyan yan kasuwa ke sauka a birnin na Islamabad.