Harin kunar bakin wake a Arewacin Bagadaza
February 25, 2016Talla
Wani daga cikin manyan jami'an 'yan sandan kasar ta Iraki ya sanar cewa, wasu mutane ne 'yan kunar bakin wake guda biyu suka tarwatsa kansu a gaban Masallacin, a unguwar Al-Shaala inda nan take mutane tara suka rasu wasu kuma 22 suka jikata cikinsu har da wani jami'in 'yan sanda.