Harin kunar bakin wake a Afghanistan ya halaka mutum biyu | Labarai | DW | 08.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin kunar bakin wake a Afghanistan ya halaka mutum biyu

Wani harin kunar bakin wake da aka kai da mota akan wani sansanin kungiyar tsaro ta NATO dake yammacin kasar Afghanistan ya yi sanadiyar mutuwar mutane 2 sannan wasu da dama suka samu raunuka. An kai harin ne a kusa da kofofin shiga sansanin na dakarun rundunar kasa da kasa ta ISAF dake aikin wanzar da zaman lafiya a birnin Herat. Wani mai gadi dan kasar da kuma wani mai wucewa harin ya rutsa da su. Harin kuwa shi ne na hudu cikin kwanaki 3 da aka kan dakarun ketare dake Afghanistan. A cikin makonnin da suka wuce ´yan tawayen kungiyar Taliban sun tsananta kai hare hare musamman akan sansanonin soji.