Harin Kunar baƙin wake a Algeria | Labarai | DW | 02.01.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin Kunar baƙin wake a Algeria

Mutane 4 ne suka rasa rayukan su

Harin kunar baƙin wake da mota ya kashe a kalla mutane 4 tare da raunana wasu 12 a ƙasar Algeria.Ɗan kunar bakin waken ya tuka motar tasa ce zuwa cikin ofishin ‚yansanda dake garin Naciria,wanda ke yankin gabashin fadar gwamnatin kasar ta Algiers.Kungiyar alqaida reshen kasar wadda keda alhakin tagwayen hare haren kunar bakin wake daya auku a ranar 11 ga watan Disamban daya kashe mutane 41,itace kazalika ta ɗauki alhakin harin na yau.Gidan talabijin din Al Arabiyya ta ruwaito wani wanda ya bayyana sunan sa kasancewa Salah Abou Mohammad,a matsayin mai magana da yawun kungiyar ,yana cewa Ɗan kunar bakin waken ya afkawa ofishin yansandan ne da kg 500 na boma bomai.