1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin Isra’ila ya janyo asarar rayukan Falasɗinawa 11.

June 14, 2006
https://p.dw.com/p/Buu5

A wata sabuwa kuma, Falasɗinawa 11 ne suka rasa rayukansu, sa’annan wasu 30 kuma suka ji rauni, sakamakon wani harin da jiragen saman yaƙin Isra’ila suka kai kan guraban Falasɗinawan a zirin Gaza. Ƙungiyar ’yan ta kifen nan ta Islamic Jihad, ta ce mayaƙanta biyu na cikin waɗanda suka rasa rayukansu a harin. Sa’o’i kaɗan kafin wannan harin dai, sai da wasu dakarun Isra’ilan suka bindige wani ɗan ƙungiyar nan ta baraden al-Aqsa, a wata musayar wutar da suka yi a garin Jenin da ke Gaɓar Yamma.

Jami’an leƙen asirin Isra’ilan, sun kutsa cikin wani asibiti ne a garin, don su cafke mutumin, wanda suke nema kamar ruwa a jallo, yayin da musayar wutar ta ɓarke.