Harin Bomb ya kashe mutane 8 a Najeriya
August 5, 2012Duk da cewar babu wanda ya ɗauki alhakin wannan harin, ana zargin ƙungiyar Ahalil sunnah lidda'awati wal jihad da aka fi sani da suna Boko Haram da kai harin. Commissionan 'yansanda na jihar Yobe, Patrick Egbmuniwe ya sanar da cewar, ɗan ƙunar baƙin waken ya tayar da boma-boman da yake ɗauke da su ne, kafin a tsayar da motar da yake ciki. Nan take sojoji shida suka mutu, da wani farar hula. Wani lokaci bayan nan ne, mutum na takwas ya rasa ransa asibiti, sakamakon rauni daya samu daga harin. Amurka dai ta ayyana ƙungiyar ta Boko haram, a matsayin ɗaya daga cikin kungiyoyin tarzoman kasa da kasa, wadda kuma keda alhakin hare-hare masu yawa da ake kaiwa a yankunan arewacin Najeriya. Wani Mazaunin unguwar gidajen gwamnati na Shagari dake Damaturu, inda aka kai harin Abdullahi Sabo, ya ce unguwar gaba ɗaya ta girgiza sakamakon karfin tarwatsewar bomb ɗin. A yanzu haka dai wasu jami'in sojin na karɓar jinya a asibiti, daga raunin wannan harin.
Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Abdullahi Tanko Bala
.