1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin Bomb ya kashe mutane 15 a Sri Lanka

Rahotanni daga kasar Sri Lanka na bayyana cewa tashin Bomb a wata motar Pasinja kirar Bus ya kashe mutane 15,tare da raunana wasu 40.Wannan tashin Bomb dai ya auku ne a kusa bakin kogin nan na yan yawon shakatawa dake garin Hikkaduwa, akudancin Sri Lankan.Idan baa mance badai a jiya ne wasu pasinjoji 6 suka gamu da ajalinsu,sakamakon tashin bomb cikin motar da suke tafiya cikinta a a yankin arewa maso gabashin Birnin Colombo.Kungiyar yan tawaye na tamil Tigers da ake zargi da kai harin dai,sun ce basu da hannu akai hare haren.