1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin Bomb a Sinai din masar

Zainab A MohammadApril 26, 2006
https://p.dw.com/p/Bu6n

Wani bomb ya fashe a wajen sansanin dakarun kiyaye zama na kasa da kasa a tsibirin Sinai dake arewacin kasar masar.Jamian tsaro dake yankin sun sanar dacewa sojoji biyu daga cikin dakrun kiyaye zaman lafiyan kasa da kasan sun samu rauni.Da farko dai jamian yansanda a masar din sun tsare mutane 10 ,wadanda ake zargi da hannu a hare haren boma bomai daya auku a Dahab,dake kasancewa wajen yawon shakatawa.Rahotanni na nuni dacewa dukkan wadanda aka cafken yan kasar ta masar ne.

Maaikatar harkokin cikin gida na masar dindai ,ta tabbatar dacewa kimanin mune 23 ne suka rasa rayukansu a harin na ranar litinin,ayayinda wasu masu yawa suka jikkata,dayawa daga cikinsu kuwa alummar kasar.$ daga cikin wadanda suka gamu da ajalinsu sakamakon harin boma boman dai yan kasashen ketare ne,ciki harda wani yaro bajamusahe mai shekaeru 10 da haihuwa.Wannan harin dai ,shine na ukun irinsa cikin tsukin watannin 18, a wannan yankin na yawon shakatawa a kasar ta Masar.