Harin Bomb a Majalisar dokokin somalia | Labarai | DW | 18.09.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin Bomb a Majalisar dokokin somalia

A kalla mutaner 4 ne suka rasa rayukansu,ayayinda masu yawa suka jikkata,sakamakon fashewar wasu ababai biyu masu nasaba da bomb a cikin harabar majalisar dokokin somalia,adaidai lokacinda shugaban gwamnatin rikon kwarya na wannan kasa ke jawabi wa yan majalisar.Fashewar boma boman guda biyu acikin motoci,ya auku ne a garin Baidoa,inda ke zama matsugunin gwamnatin riko na somalian,harin da kuma ya kone sauran motoci dake kewayen wadanda boma boman suka tarwatse a cikinsu.jamian kasar dai sun sanar da cewa shugaban kasa abdullahi Yusuf Ahmed ya tsira ba tare da samun rauni ba,sai da yawa daga cikin sauran jamiaan sa sun jikkta.A yau din dai anasaran shugaban na Somalia,zai nemi amincewar yan majalisara kasar dangane da sabbin yan majalisar zartarwa da yake neman nadawa,a wannan gwamnati dake da madafan iko kalilan a wannan kasa dake fama da rigingimu.

 • Kwanan wata 18.09.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu5P
 • Kwanan wata 18.09.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu5P